1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Yakin Gaza ya yi tasiri a nasarar Trump da Biden a Michigan

February 28, 2024

A yayin da wasu 'yan jam'iyyar Democrate a Michigan a Amurka suka sha alwashin yakar shugaba Joe Biden sakamakon rawar da yake takawa a yakin Gaza, Biden ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar Democrate cikin sauki.

https://p.dw.com/p/4cxsl
Rumfar zabe a Michigan Amurka
Rumfar zabe a Michigan Amurka Hoto: Mostafa Bassim/Anadolu/picture alliance

Shima tsohon shugaban kasar Donald Trump ya lashe zaben fidda gwanin a jam'iyyarsa ta Republican a Michigan, da gagarumar rinjaye kan 'yar takarar da take hamayya da shi Nikki Haley, wadda kuma ita ce 'yar takara daya tilo da ta rage da Trump ya kayar a zaben fidda gwani na Republican.

Karin bayani:Biden ya sanar da kudurin yin takara a 2024

Jihar ta Michigan da ke dubban Amurkawan da ke tsatso da Larabawa sun lalata galibin kuri'unsu na zaben fidda gwanin jam'iyyar Democrate mai mulki domin nuna adawa kan rawar da Biden yake takawa a yakin Zirin Gaza. Kuri'u sama da dubu 58,000 ne aka lalatasu domin nuna fushi kan abin da ke faruwa a Gaza.

Karin bayani:Biden na zawarcin kuri'un Larabawan kasar