1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Zaben Amurka: Biden na zawarcin kuri'un Larabawan kasar

February 22, 2024

Amurkawa da ke da tsotso da kasashen Larabawa sun sha alwashin kalubalantar shugaban kasar Joe Biden a zaben da ke tafe na watan Nuwamba, sakamakon rawar da ya taka wajen goyon bayan Isra'ila a yakin Gaza.

https://p.dw.com/p/4cj5y
Masallacin Wadea Al-Fayoume da ke Illinois a Amurka
Masallacin Wadea Al-Fayoume da ke Illinois a AmurkaHoto: Jacek Boczarski/Anadolu/picture alliance

Dubban Larabawan Amurkan da galibinsu ke yankin Detroit a jihar Michigan na fadakar da mazauna yankin a shaguna da masallatai a harsunan turanci da larabci wajen kauracewa zaben Biden.

Samra'a Luqman, na daga cikin wadanda suke gangamin wayar da kan mutane a al'amuran siyasa, ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa ya na da ruwa da tsaki a kisan kare dangin, kuma shi ke daukar nauyi.

Gwamnatin Biden  na ci gaba da kokarin shawo kan Larabawan Amurka da kuma Musulmi kan cewa Amurka na cike da takaicin abin da Benjamin Netanyahu ke aikatawa a Zirin Gaza.