IS ta kashe rayuka sama da 100 | Labarai | DW | 23.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

IS ta kashe rayuka sama da 100

Rahotanni daga Syria na cewa sama da mutane 100 ne mayakan IS suka halaka cikin wannan watan na Oktoba, yayin suka fuskanci rushewar daularsu.

Sama da mutane 100 ne mayakan IS suka halaka cikin wannan watan na Oktoba, yayin suka fuskanci rushewar daularsu da sojojin gwamnati. suka tasanwa yi a birnin Raqqa. Kungiyar kare hakkin Siriyawa ta Syrian Observatory for Human Rights wadda ke da cibiya a Birtaniya, ta ce mayakan sun kashe mutanen ne a wani yanki na Qaryatain, kafin kwace iko da dakarun gwamnati suka yi.

A makon da ya gabata ne dai kungiyar ta rasa babbar tungarsu a Syria wato Raqqa a dai dai kuma lokacin da suke fusknatar zafi daga ita ma Iraki mai makwabtaka da kasar. Alkaluma sun tabbatar da cewa sun kashe akalla mutane 116 cikin kwanaki 20, saboda zargin mutanen da bai wa sojoji Bayanai. Cikin shekara ta 2015 ne dai kungiyar ta IS ta kama birnin na Raqqa.