Iran ta ce dole a bar gwamnatin Siriya ta ci gaba da mulki | Labarai | DW | 28.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta ce dole a bar gwamnatin Siriya ta ci gaba da mulki

A cewar shugaba Hassan Rouhani murkushe mayakan na IS shi ya kamata a ba wa fifiko kafin daga bisani a koma ga batun sauyin mulki a kasar ta Siriya.

USA Hassan Rouhani bei der UN in New York

Shugaba Hassan Rouhani na Iran

Shugaba Hassan Rouhani na kasar Iran ya yi gargadin cewa dole a bar mahukunta a kasar Siriya su ci gaba da rike madafun iko muddin ana son ganin bayan kungiyar IS ko kuma kasar ta fada hannun mayakan.

Shugaba Rouhani da ya ke halartar taron koli na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York na Amirka, a ranar Lahadi ya bayyana cewa kokarin murkushe mayakan na IS shi ya kamata a bawa fifiko kafin daga bisani a koma wa batun sauyin mulki a kasar ta Siriya.

A jawabinsa ga taron malaman jami'a da 'yan jarida ya ce muddin muradin da ake da shi shi ne a murkushe ayyukan na ta'addanci, to ya zama dole kada a bude wata kofa da za ta sanya gwamnatin ta mahukuntan birnin Damascus ta samu rauni, dole a bata dama ta ci gaba da jan ragama ta yakar mayakan na IS.

Wannan jawabi na shugaba Rouhani na zuwa ne a daidai lokacin da cece-kucen diplomasiya ke kara zafi kan rikicin na Siriya, da tsawon shekaru hudu da ya kwashe ya yi sanadin rasa rayukan mutane 240,000 yayin da wasu dubbai aka tilasta musu yin hijira zuwa kasashen Turai.