Iran ta ayyana ranar makoki | Labarai | DW | 14.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta ayyana ranar makoki

Kasar Irani ta ayyana ranar Talata a matsayin ranar zaman makoki a hukumance domin nuna jimamin mutuwar mutanen da girgigar kasa ta rufta da su a yankunan kasar masu tsaunuka da ke kan iyaka da Iraki.

Hukumomin Iran sun kuma yi addu'a ga ga iyalan mamatan, da wadandan suka jikata da ayanzu ke gadajen asibiti sakamakon girgizar kasar. Alkaluman gwamnati na cewa adadin mutanen da suka mutu ya kai mutune 430, yayin da sama da mutane dubu 7,000 aka tabbatar suna karbar jinya.

Girgizar kasar mai karfin maki 7.3 ta fi muni ne a lardunan yammacin kasar, sai dai an samu rahotannin mutuwar mutane takwas tare da jikkata mutane 500 a makociyar kasar Iraki. Ana sa ran shugaban kasar Iran Hassan Rowhani zai ziyarci yankunan da girgizar kasar ta auku.Girgizar kasa ta kashe mutane 200 a Iran

DW.COM