1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girgizar kasa ta kashe mutane 200 a Iran

Abdul-raheem Hassan
November 13, 2017

Alakaluma daga hukumomi sun ce adadin mutanen da suka mutu a girgizar kasar da ta auku a ranar Lahadi ya haura 200, yayin da wasu mutane sama da 1,000 ke karbar magani a asibitocin kasar.

https://p.dw.com/p/2nVU6
Iran Erdbeben
Hoto: Getty Images/AFP/P. Pakizeh

Girgizar kasar mai karfin maki 7.3 ta fi muni a lardunan Kermanshah da Illam da ke kan iyaka da Arewacin Iraki, hukumomi kiwon lafiya a kasar na fargabar samun karuwar adadin wanda suka rasu. Jami'ai sun ce an samun yawaitar ruftawar gidajen laka da dama wanda ya kara munana lamarin.

Girgizar kasar ta haddasa tsagewar kasa a kusa da birnin Halabja na yankin kuradawa da ke kasar Iraki jim kadan bayan afkuwar girgizar kasar inda aka samu rahotannin mutuwar mutane shida. Amma hukumoin gwamnatin Iraki ba su ba da bayanai  kan asarar da girgizar kasar ta haddasa a hukumance ba kawo yanzu.

Masu ayyukan ceto na kokawa da rashin samun damar gudanar da ayyuka yadda ya dace, sakamakon rashin hasken wutan lantarki da katsewar manyan tituna a birnin da girgizar kasar ta afku, kazalika girgizar kasar ta haddasa karancin ruwan sha a yankunan da abin ya faru.