Mene ne hadarin kai hari kan kasar Iran?
January 21, 2026
Cikin kwanakin da suka gabata Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi alkawarin taimakon masu zanga-zanga na kasar Iran, saboda amfani da karfi da gwamnati take yi kan masu zanga-zangar a titunan kasar. Amma daga bisani wanna taimakon bai yuwu ba. Sannan Trump ya ce bai yarda cewa akwai tunanin kashe mutane masu yawa ba, saboda zanga-zangar.
Sai dai wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta Iran mai mazauni a Amurka ta ce masu zanga-zanga 3,919 aka tabbatar sun halaka sakamakon matakin na hukumomin Iran. Taunnawar diflomasiyya tsakanin Amurka ta kasashen Larabawa irin Saudiyya, da Masar, da Oman, da Katar, sun shawo kan Amurka na fasa kai taimakon ga masu zanga-zangar na Iran.
Pauline Raabe da ke cibiyar kula da lamuran Gabas ta Tsakiya a birnin Berlin na Jamus tana ganin tunanin yuwuwar bazuwar zanga-zangar zuwa kasashe makwabta ya saka kasashen ba su goyi bayan Amurka ta kai farmaki a Iran ba.
Kasashen yankin Gulf suna tsoron rikicin na Iran zai iya fadada ya tabarbara lamura a yankin, ga kuma yuwuwar haifar da 'yan gudun hijira. Eckart Woertz masanin harkokin siyasa kana daraktan cibiyar nazarin harkokin Gabas ta Tsakiya da ke birnin Hamburg na Jamus shi ma yana da irin wannan ra'ayi na taka tsantsan daga kasashen Larabawa kan duk wani hari kan kasar Iran.
Ita kanta kasar Iran tana iya daukan wasu matakai idan rikicin ya fadada wajen tsoshe hanyoyin kasuwanci ta ruwan yankin, kana akwai karnukan farautansu 'yan Houthi da ke Yemen wadanda suna iya dagula tafiye-tafiye jiragen ruwa a tekun Bahar Maliya. Akwai masu tunanin cewa ba sai an yi amfani da karfi ba, idan lokacin faduwar gwamnatin Iran ya zo, ganin irin matsalolin da suka yi mata katutu.