Iraki ta taka wa Amirka birki | Siyasa | DW | 24.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Iraki ta taka wa Amirka birki

Gwamnatin Iraki ta mayar da martani ga Amirka kan kiran da ta yi na sallamar mayakan sa-kai na kasar Iran da suka taimaka bisa yakin dakile kungiyar IS da ta haddasa mutuwar daruruwan mutane.

Tuni dai wannan batu ya haifar da cece-kuce a kasar, za a iya cewa sannu a hankali kasar Iraki  na daukar matakan kwance kanta daga mugun kullin da Amirka tai mata, bayan da ta samu nasarar murkushe kungiyar ‘yan ta'addan IS, ta kuma kwace birnin Kirkuk mai dimbin arzikin man fetir daga hannun mayakan Kurdawa ‘yan aware dake da kyakyawar hulda da Amirka, yanzu ta tashi haikan wajen kyautata alakarta da Saudiya wacce a can baya basa ga maciji da juna, ta kuma kulla sabbin yarjeniyoyin tsaro da kasashen Iran da Turkiya, wadanda ke da tsamin dangantaka da Amirkan a wani mataki da masana ke kallo a matsayin  sabon ‘yancin kai ga kasar Iraki na dogaro da kanta.

Tuni dai Amirka ta soma jan kunnan gwamnatin Iraki kan sabbin matakan da take dauka, sakataren Amirka Rex Tillerson dake shirin kai ziyara a Irakin ya nemi gwamnatin kasar da ta dauki mataki na korar illahirin mayakan sa kai ‘yan kasar Iran da suka tallafawa dakarunta fatattakar ‘yan IS, batun da firaiministan Irakin Haidar al-Abadi ya kare matakin.

 A baya Amirka karkashin gwamnatin Barack Obama ta mika jinjina ga mayakan na ‘yan Shi'a inda jakadanta a Irakin Stev Worker na wancan lokacin ya kwatanta su da zaratan murkushe ‘yan ta'adda. A yayin da wasu ‘yan kasar ta Iraki ke yabawa da wannan tsiwar da Firaiministan ya yi wa Amurka, wasu daga cikin al'umma na ganin ya debo da zafi inda suka nemi ya yi taka tsantsan, musammama matakin kulla sabbin kawancen da kasashen da a shirye suke su raba gari da kowa don samun yardar Amirka.