Iraki na fuskantar barazana fadawa cikin yakin basasa | Labarai | DW | 02.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iraki na fuskantar barazana fadawa cikin yakin basasa

Wani rahoto da ma´aikatar harkokin wajen Amirka ta mikawa majalisun dokokin kasar ya yi nuni da cewa rikicin Iraqi na da dukkan alamu na zama wani yakin basasa, to amma har yanzu da akwai yiwuwar hana iya hana hakan aukuwa. Rundunar sojin Amirka ta bayyana tabarbarewar halin tsaro a Iraqi da cewa ya fi na ko wane lokaci yin muni tun bayan da sojin Amirka suka mamaye kasar sama da shekru 3 da suka wuce. Rundunar ta ce a cikin watanni 3 da suka wuce an samu karuwar yawan hare hare a cikin kasar da misalin kashi daya cikin hudu inda a kowanemako ake kai hare hare kusan 800. Yayin da yawan ´yan Iraqi dake mutuwa sakamakon tashe tashen hankula ya ninka har sau biyu izuwa mutum 120 a kowace ranar Allah ta-ala. Babbar baranaza ga wanzuwar zaman lafiya a kasar shi ne rikici tsakanin ´yan shi´a da ´yan sunni, inji rahoton.