1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Adamawa: An yanka ta tashi

April 16, 2023

Hukumar zaben Najeriya INEC, ta yi watsi da sakamakon zaben gwamna da aka bayyana a jihar Adamawa, tana mai bayyana shi a matsayin ba karbabbe ba.

https://p.dw.com/p/4Q9TT
Nigeria | Nach den Wahlen | Mahmood Yakubu
Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture alliance

INEC din ta kuma dakatar da aikin tattara sakamakon zaben cike gurbi da aka yi, wanda kwamishinan zaben ya ayyana Sanata Aisha Ahmed Binani ta jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe shi. Tuni ma ta umurci kwamshinan zaben Jihar ta Adamawa da sauran baturan zaben da su hallara a shelkwatarta da ke Abuja babban birnin Najeriyar.