Indiya ta hallaka ′yan bindiga da suka kai hari | Labarai | DW | 03.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Indiya ta hallaka 'yan bindiga da suka kai hari

Indiya ta ce jami'an tsaronta sun yi nasarar hallaka mutane biyu daga sauran mambobin rukunin 'yan bindigar da suka kaddamar da hari a sansanin sojojin kasar na Pathankot na cikin jihar Pendjab

Wata majiyar 'yan sanda ta kasar Indiya ta ce a wannan Lahadi jami'an tsaron kasar sun yi nasarar hallaka mutane biyu na sauran mambobin rukunin 'yan bindigar da suka kaddamar da hari a sansanin sojojin kasar na Pathankot na cikin jihar Pendjab da ke a nisan kilomita 50 da kan iyakar kasar ta Indiya da makobciyarta ta Pakistan.

An kashe 'yan bindigar biyu ne a lokacin wata fafatawa da aka yi da su a wani filin jirgin sama na arewacin kasar.

A jimilce sojojin gwamnati bakwai da kuma 'yan bindiga shida suka rasu a cikin wannan harin da wasu 'yan bindiga da ake zaton mambobin wata kungiyar masu tsananin kishin addini ta kasar Pakistan ce mai suna Jaish-e-Mohammed suka kawo shi a cikin daren Jumma'a washe garin Asabar.

Yanzu haka dai jami'an tsaro na ci gaba da yin binciken kokop a sansanin sojin na Pathankot domin tabbatar da cewa babu sauran 'yan bindigar da suka boye a cikinsa.