1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin daidaita jinsi a siyasar Kenya

August 5, 2022

Duk da tanadin kundin tsarin mulki kan daidaita jinsi, maza na ci gaba da mamaye fagen siyasar kasar Kenya, duk da fafutukar samun gurbi a fagen siyasa da mata da dama ke yi.

https://p.dw.com/p/4FAvu
Hoton 'yan takara a zaben shugaban kasar Kenya
Hoton 'yan takara a zaben shugaban kasar KenyaHoto: Yasuyoshi Chiba/AFP

Kundin tsarin mulkin kasar Kenya ya tanadar wa mata kashi daya cikin uku a fannoni daban-daban na mukaman gwamnati , a yayin da al'ummar Kenya ke shirin kada kuri'a zaben shugaban kasa da na majalisa a ranar tara ga watan Agusta, babu mata 'yan takara da yawa da za a iya jefa wa kuri'a daga cikin 'yan takara dubu goma 16, kasa da dubu 2 ne kawai mata.

Cimma burin da kundin tsarin mulki ya tanada abu ne da yake da matukar wahala. A Kenya ce kasa mafi karancin mata a fagen siyasa a gabashin Afrika, inda matan suke da kashi 23 daga cikin 100 na kujerun majalisa.

Karin Bayani: Kalubale mata Ungozoma da ayyukansu

Mercy Wambui na daukar nauyin yakin neman zaben wata 'yar takara, na da yakinin abubuwa sun fara canzawa nan da gaba."Muna samun tallafi mai kyau daga wurin mutane da suka fahimceta suka ji takaitaccen tarihinta suka kuma san abinda zata iya".

Ana dakon ganin sauyin yanayi a siyasar Kenya, dan takarar shugaban kasa Raila Odinga ya nada tsohuwar ministar shari'a Martha Karua a matsayin mataimakiyarsa a zabe mai zuwa. Hakan zai sa Karua ta zama mace mataimakiyar shugaban kasa ta farko a kenya idan har Odinga yaci zabe.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan rabin matan Kenya sun taba fuskantar duka ko fyade daga mazajensu, bugu da kari kashi 23 a matan kasar an musu aure ne a kananan shekarun ko baya ga rashin shiga a dama da su a fagen siyasa.

Karin Bayani:  Fada a majalisar dokokin Kenya

Masu cin zarafin mata na anfani da kafafen sada zumunta, Esther Passaris 'yar siyasa ce mai wakiltar mazabar birnin Nairobi, ta sha zagi bayan da ta yi wani rubutu akan marigayi mahaifinta

Maza 'yan siyasa kan yi watsi da dokokin da kotu kan tanadi na kudin tsarin mulki don su cimma burinsu. A shekarar 2018 'yan siyasa sun kauracewa zaben majalisa wanda zai iya bawa mata damar samun gurabe akalla daya cikin uku a majalisar dattawa. Tun daga lokacin ba'a samu wani yunkuri na karfafa gwiwar daidaton jinsi a majalisar dokoki ba.