1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya:'Yan majalisa sun bai wa hamta iska

Abdourahamane Hassane
December 29, 2021

'Yan majalisar dokoki a Kenya sun bai wa hamata isaka a zauran majalisar a sa'ilin da suke  tattaunawa kan wani kudirin doka a kan  tsarin jam'iyyun siyasa.

https://p.dw.com/p/44xzR
Parlamentsabstimmung Kenia Nairobi Wahlen Parlament
Hoto: AP

'Yan majalisar akalla guda biyu sun rika yin  dambe a cikin zauren har sai da shugaban majalisar ya dakatar da zaman tattaunawar. Gidan talbijan na Kenya ya nuno daya daga cikin masu fadan dan majalisar da jini jina-jina a fuskarsa. Fadan ya barke ne a kan kudirin dokar da ke yin kwaskwarima wajen tsara tafiyar jam'iyyun siyasa da irin kawancen da suke iya yi. Masu adawa da kudirin na zargin cewar shugaba Uhuru Kenyatta, na iya yin amfani da kudirin domin yin kawance da tsohon abokin adawarsa Rail Odinga a zabukan gama gari da za a yi a cikin watan Augustan da ke tafe.