EU na son sanin matsayar Birtaniya
March 16, 2019Talla
A wani batu mai kama da tsakiyar da ba ruwa ga firaministar Birtaniya Theresa May, shugabannin kungiyar Tarayyar Turai sun bukaci sanin inda Birtaniya ta dosa kamin su yanke shawarar daga mata kafa na ficewa daga kungiyar.
Mrs May na cikin tsaka mai wuya ganin yadda kudirinta kan matsayar kasar bayan ficewa daga EU ya gaza samun nasara a majalisar dokokin kasar.
A ranar 29 ga wannan wata na Maris aka shirya ficewar Birtaniya daga kungiyar EU a hukumance idan har shugabannin kungiyar ba su tsawaita wa'adin ficewar ba, batun da zai mamaye taron kungiyar a mako mai zuwa a Brussels. Birtaniya na fatan tsawaita ficewarta daga kungiyar zuwa watan Yuni bayan da ta shafe shekaru biyu tana kokarin cimma matsaya.