1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nazarin yanayin tattalin arzikin Afirka

Ramatu Garba Baba
March 10, 2022

Asusun Lamuni na Duniya na duba yiyuwar tallafa wa kasashen Afirka da tattalin arzikinsu ke kokarin durkushewa a sakamakon yakin da ake gwabzawa a tsakanin Rasha da Ukraine.

https://p.dw.com/p/48J2l
Washington IWF Logo Symbolbild
Hoto: Getty Images/AFP/M. Ngan

Matsin tattalin arziki da hauhawar farashin abinci dama tsadar man fetur a kasashen Afirka, ya kara ta'azzara ne a sakamakon yakin Rasha da Ukraine in ji Asusun bayar da Lamuni na Duniya IMF. Wannan ya sa asusun soma nazari, domin duba yiyuwar tallafa wa kasashen, don rage radaddin da yakin ya haifar ga tattalin arzikin nahiyar.

Tun bayan barkewar yakin na fiye da makonni biyu, kasashen na Afirka kamar sauran kasashen duniya, suka soma fuskantar matsi dama koma baya, musanman a fannin masu zuwa yawon bude ido da fannin hada-hadar musayar kudaden waje.