Hukuncin kisa kan sojojin Najeriya | Labarai | DW | 18.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukuncin kisa kan sojojin Najeriya

A Najeriya kotu ta yankewa wasu sojojin kasar 54 hukuncin kisa bisa samunsu da ta ce ta yi da laifin kin bin umurni ta hanyar kin amincewa su yaki mayakan kungiyar Boko Haram.

Hukuncin da kotun sojojin kasar ta ce ta sami sojojin da laiyanke dai ya biyo bayan tuhumar da ake musu wadda ke da nasaba da kin amincewa a tura su zuwa garuruwan nan uku da jami'an tsaron Najeriyar suka kwace daga hannun mayakan na Boko Haram, bayan da kungiyar ta kwace garuruwan a cikin watan Agustan da ya gabata wanda ta bayyana da tsoro. Lauyan da ke kare sojojin da aka yankewa hukuncin Femi Falana, ya ce kotun ta kama su da laifi tare da yanke musu hukuncin kisa. Jami'an tsaron Najeriyar dai na korafin cewa basu da isassun makamai da kayan aiki da za su iya tunkarar mayakan na Boko Haram. Kawo yanzu dubun-dubatar mutane ne suka rasa rayukansu a Tarayyar Najeriyar yayin da wasu sama da miliyan guda suka kauracewa gidajensu a yakin da mahukuntan kasar suka kwashe tsahon shekaru biyar suna yi da 'yan kungiyar Boko Haram din da ke gwagwarmaya da makamai a kasar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu