1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar: Hukuncin kisa kan mutane 37

Abdul-raheem Hassan
March 2, 2020

Wata kotu a kasar Masar ta yanke hukuncin kisa kan wani hatsabibin mutum da wasu 37 bayan samunsu da laifukan ta'addanci da kuma taimaka wa kungiyar IS.

https://p.dw.com/p/3YkQo
Symbolbild Ägypten Gefängnis
Hoto: picture-alliance/AA

Hisham el-Ashmawi da kotun ta kwatanta a matayin shugaban kungiyoyin tada kayar baya, tsohon shugaban bataliyar sojojin da ke biyayya ga Janar  Khalifa Haftar ne a kasar Libiya.

Sauran mutanen da aka yanke wa hukuncin kisan, suna cikin mutane 200 da gwamnatin Masar ke zargi da kai hare-hare kusan 50 da ya yi sanadiyar rayukan fararen hula da 'yan sanda.

Masar ta sha fuskantar hare-haren daga kungiyoyin 'yan tawaye da suka addabi arewacin Sinai da yankunan da ke yammacin Hamada. Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil Adama na sukan irin wannan kisan da gwamnatin ke yi.