Hukumar NHRC ta Najeriya ta fitar da rahoto | Labarai | DW | 13.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar NHRC ta Najeriya ta fitar da rahoto

A kalla dai mutane 58 ne suka rasu daga watan Disamba kawo yanzu, sakamakon rikice-rikicen siyasa a Najeriya a cewar Hukumar kare hakin dan Adama ta kasa NHRC.

Hukumar ta fitar da wannan rahoto ne a wannan Jumma'a tare da yin Allah wadai da yadda wasu 'yan siyasa ke amfani da miyagun kalammai da ke tayar da hankulan al'umma. Hukumar ta NHRC ta ce a tsawon kwanaki 50 tun daga watan na Disamba da ya gabata, ta samu rahotanni kuma ta yi bincike kan rikice-rikice da suka shafi siyasa a kalla guda 60 wadanda gabaki dayansu ne suka haddasa rasuwar mutanen 58 wasu da dama suka samu raunuka.

Rahoton na hukumar kare hakin dan Adama ta Tarayyar Najeriya ya ce wadannan rigingimu an samesu ne a cikin jihohi 22 daga cikin 36 na kasar, inda ta ce muddin dai ba'a dauki wasu matakai ba tun yanzu, to zabubukan kasar na 2015 na da manyan hadaruruka na samun rigingimu a ciki.