1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kada kuri'ar amincewa da sabuwar hukumar EU

Mohammad Nasiru Awal AH
November 27, 2019

Majalisar dokokin Turai ta kada kuri'ar amincewa da sabuwar hukumar Ursula von der Leyen, bayan watanni na rashin tabbas. A ranar 1 ga watan Disamba sabuwar hukumar za ta fara aiki.

https://p.dw.com/p/3Tq0F
Sitzung Europäisches Parlament - Wahl EU-Kommission Ursula von der Leyen
Hoto: Reuters/V. Kessler

Shugabar Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai mai jiran gado, Ursula von der Leyen ta fada a wannan Laraba cewa yaki da sauyin yanayi na zama babban kalubale saboda haka za ta tabbatar da an ware kudade da za su taimaka wajen rage amfani da makamashi irinsu kwal da mai da kuma rage fid da hayaki mai gurbata yanayi.

Von der Leyen ta fada wa majalisar dokokin Turai da ke birnin Strasbourg na kasar Faransa, gabanin kada kuri'ar karshe ta tabbatar da ita a matsayin shugabar hukumar EU cewa ba bu sauran lokaci da za a bata wajen yaki da sauyin yanayi ba.

"Idan akwai wani fannin guda daya da duniya ke matukar bukatar shugabancinmu to shi ne na kare muhalli. Wannan muhimmin batu ne ga Turai da duniya baki daya."

Yanzu haka dai 'yan majalisar Turai sun kada kuri'ar share wa von der Leyen hanyar kama aiki a matsayin sabuwar shugabar Hukumar EU a ranar daya ga watan Disamba, inda wakilai 461 suka ba ta goyon baya yayin da 157 suka nuna rashin amincewa sannan 89 suka yi rowar kuri'unsu.