1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hubbasar da hukumomi ke yi na wadata al'umma da ruwan sha

March 21, 2014

A yayin da ake bukin zagayowar ranar ruwa ta duniya, al'ummar jihar Damagaram a Nijar, na kokawa game da rashin wadataccen ruwan.

https://p.dw.com/p/1BU7v
Flüchtlingscamp Menawo
Hoto: DW/M. Kindzeka

A yayin da ake gudanar da shagulgulan zagayowar ranar 22.03., wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin ruwa, a yankin Damagaram na Jamhuriyar Nijar tsugunu bata kare ba, inda a yanzu haka adadin ruwan da zai wadaci al'ummar birnin Damagaram ya haura lita miliyan 16 a kulum ya kasance wani babban kalubale ga hukumomi. A dangane da wannan matsala dai, tuni kwararrun ma'aikatar gidan ruwa suka gayyaci kungiyoyin fararen hula don nuna masu girman matsalar.

Shekara daya na bin daya dai kimanin shekaru 40 ne al'ummar birnin na Damagaram ke fama da matsalar ruwan sha, wacce a shekaru bakwai baya, a zamanin Jamhuriya ta biyar, talakawan ke ganin ta kama hanyar zama tarihi ga batun matsalar, wacce a lokacin yakin neman zabe ne kawai magabatan kasar da 'yan siyasa ke nuna damuwarsu da zaran sun ci zabe, to sai ta 'yan mota.

Tschad - Leben am Tschadsee
Mazauna tafkin ChadiHoto: picture-alliance/ dpa

Dalilan rashin wadata yankin Damagaram da ruwan sha

A daura da wannan matsala ta rashin samun isassun ruwan sha, hukumar gidan ruwa wacce jama'a ke zargin tana da hannu wajen fadada matsalar, a wani mataki na ramuwar gayya tuni ta bullo da wani tsarin rabon ruwa daga wannan unguwa zuwa waccan inda a karshe ta gayaci wakilan kungiyoyin fararen fulla don nuna masu gaskiyar lamarin a wuraren da suke tuttudo da ruwan kamar gogo da kuma Arunguza. Malam Adamu shi ne wakilin kamfanin gidan ruwa na garin Gogo, matsalolin da suke fuskanta ya bayyana ga ''yan farar hular.

To ko yaya 'yan farar hular ke fassara girman matsalar, ganin sun gane ma idanunsu abin da ke wakana a wuraren matattarar ruwan jihar? Ga dai yadda ta bakin wasu daga cikin wakilan kungiyoyin fararen hular daban daban da suka hada da su Malam Tanko da Abdulmajid daga MPPAD.

Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Shugaba Mahamadou Issoufou na NijarHoto: picture alliance / dpa

Fatan samun ruwan famfo a Damagaram

A yanzu haka dai a wasu unguwanni jama'a sun manta da su gana da ruwan famfo da rana tsaka, ko da suna cikin tsarin rabon ruwa da akafi sani da suna Delestage, inda tuni ma dai matsalar ta fara zama jiki. Abin jira a gani dai shi ne lokacin da shugaban kasa Isufu Mahamadu zai dauka na kamalla aikin jan ruwa da zai kwashe kimanin watanni 30, ko an bayyana cewar bafatake ya dace da tsinkewar kaya a gindin kaba.

Mawallafi : Larwana Malam Hami
Edita : Saleh Umar Saleh