HRW: Rikicin Boko Haram ya karu a Najeriya a 2018
January 17, 2019Talla
Kungiyar ta Human Right Watch ta ce gazawar gwamnatin Najeriya na bada cikakkiyar kariya ga jama'a ya nuna wagegen gibi wajen tabbatar da tsaro.
Rahoton ya kara da cewa an kashe mutane akalla 1, 200 yayin da wasu mutanen kimanin 2000 kuma suka tagaiyara a shekarar ta 2018 a cigaba da rikicin Boko Haram da ya dauki kusan shekaru tara ana fama da shi a arewa maso gabashin kasar.
Satar mutane da hare haren kunar bakin wake da harin 'yan Boko Haram akan fararen hula sun cigaba da aukuwa duk da ikrarin sojojin gwamnati na murkushe 'yan kungiyar ta Boko Haram.