A wata tattaunawa da DW Hausa ta yi da Dakta Yunusa Tanko da ya kasance hadimin tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya na jam'iyyar Labour Party Peter Obi, yayin ziyarar da ya kawo Jamus ya bayyana kokarin da suke yi na kawo sauyi a Najeriya tare da kalubalantar wasu tuhume-tuhume da ake yi wa Peter Obi din.