Himma dai Matasa: Matashin tela a Sokoto | Himma dai Matasa | DW | 30.09.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Himma dai Matasa: Matashin tela a Sokoto

Wani matashi da ke shekarar karshe a jami'ar Usmanu Danfodiyo ta Sokoto ya rungumi sana'ar dinkunan maza da mata irin na zamani a wani mataki na kaucewa fadawa rashin aikin yi bayan kammala jami'a.

Nigeria HdM: Sokoto Tailor

Abubakar Abdulrahman matashin tela a jihar Sokoto da ke Najeriya

Matashi Abubakar Abdulrahman wanda ya je jihar ta Sokoto karatu da kuma yanzu haka yake shekarar karshe a jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoton, ya ce ya kama sana'ar ne sakamkon tsaikon da aka samu na karatu saboda annobar cutar coronavirus, abin da ya ce ya sanya shi mayar da hankalinsa ga kara zamanantar  da sana'ar dinki zuwa nau'i na zamani.

Matashin dai ya bayyana cewa ya shafe tsawon lokaci yana tinani da kuma kirkirar wannan sana'ar, inda hakan ya taimaka masa ainun har ma sannu a hankali ya samu damar bude kanfaninsa mai suna: "AA Funtua Clothing." 

To amma kuma wani abun sha'awa da ake ganin matashin ya kawo, bai wucewa yadda yake samar da gurabun ayukkan yi ga matasan da suka fito daga jihohin Niger da Kano da kuma Kaduna ba. Koda yake matashin ya bayyana irin nasarori da kuma kalubalen da yake fuskanta a sana'ar, amma ya ce yana ta kokarin shawo kan kalubalen.