1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Matashi da ya kirkiri injin kyankyasar kaji

March 7, 2022

Matashi Muhammad Usman ya soma kirkirar injuna da ciki har dana kyankyasar kaji bayan ya kamalla karatunsa na Diploma a jahar Katsina da ke Arewacin Najeriya.

https://p.dw.com/p/488jD
Frankreich | Geflügelfarm in Tennie
Hoto: Vincent Isore/IP3press/imago images

A Arewacin Najeriya, wani matashi a jihar Katsina da ya kammala karatun Diploma babu kuma aikin yi, ya kirkiro injin kyankyasar kaji me amfani da wuta da gas da kuma hasken rana. Matashin ya ce, yanzu haka ya kera inji sama da 30 Baya ga haka, ya dauki matasa kusan goma aiki.

Daya daga cikin injinan kyankyasar kajin wanda a lokacin da DW ta ziyarci wurin, ana cikin kyankyasar kajin kuma da hasken rana. Usman ya samu nasarori a sakamakon kirkiro wannan inji kyankyasar kaji me amfani da hasken rana da kuma gas.

Sai dai matashin ya ce, tsadar kayayyakin hada injin kyankyasar kajin shi ne babban kalubalen da yake fuskanta kana ya yi kira ga matasa da suyi amfani da fasahar su wajan cigaban kasa.

Alh Ya'u Umar Gwajo-gwajo shi ne Shugaban Kungiyar Manoma jihar Katsina Kuma Yana da cikin wadanda suka sai wannan injin kyankyasar kaji me amfani da gas da kuma hasken rana wanda yanzu haka yana amfani da shi.