1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Matashi mai sana'ar sayar da burodi

August 25, 2021

Wani matashi a jihar Kaduna da ke Najeriya, ya yi watsi da aikin gwamnati da kuma banki bayan ya kammala hidimar kasa tare da rungumi sana'ar sayar da burodi a kan  babur.

https://p.dw.com/p/3zTWU
Frankreich Lille | Bäckerei | Baguette und Brot
Sana'ar sayar da burodiHoto: David Hughes/robertharding/picture-alliance

Matashin mai suna Ali Dahiru Garga dai, na shiga lungu da sako domin sayar da burodin nasa. Ya ce ya dade yana neman aiki amma a karshe sai yaga yana batawa kansaa lokaci ne, hakan ya sanya ya fara wannan sana'ar. Ali ya ce ya fara sana'ar sayar da burodi a kan babur da burodi 50, to amma yanzu a kowace rana yana yin safarar guda 400. Ya ce ya samu nasarori masu tarin yawa, koda yake akwai kalubalen da ba za a rasa ba. Matashin ya kuma shawarci 'yan uwansa matasa, a kan su tashi tsaye domin neman na kansu.