Nijar: Matashiya mai yin cakulan
January 15, 2020Talla
Ita dai wannan matashiya mai kimanin shekaru 25 da haihuwa mai suna Ajata Samba duk da kasancewarta 'yar jami'a, ta dukufa wajen sarrafa kwakwa da madara domin samar da alwar mai dandanon cakulan wanda yara da manya ke saye saboda dadin dandanonta. Matashiyar dai ta ce daman ita burinta tun tana 'yar karama shi ne ta dogara da kanta. A halin yanzu dai ana iya cewa sannu a hankali matasa da suka kammala karatunsu wasu ma kafin su kammalawa baki daya na nemarwa kansu mafita, abin da ake yi wa kallo a matsayin yadda matasan ke kara sanin inda yake yi musu ciwo sabanin shekarun baya.