Bai wa matasa horon kwallon kafa a Jos
July 10, 2019Wannan matashi mai suna Adamu Babawo wanda akafi sani da Babawo Lecturer, ya ce tun yana karami ya ke da sha'awar ganin kwallon kafa ta zame masa hanyar dogoro ta rayuwa, don haka ya fuskanci wassan kwallon bayan ya kammala karatu, inda yanzu haka yake da lasisin Hukumar Wasan Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) domin rika fitar da 'yan wasa zuwa kasashen Turai, kuma wasu daga cikinsu su kan sami zuwa kasashen na Turai domin buga kwallon kafa. Da tallafin wannan cibiya ta horar da matasa wasan kwallo da ke Jos din, yanzu matasa masu basirar wasan kwallon kafa kan sami horo, inda sukan zamanto masu dogaro da kai a rayuwa bayan sun gama samun horon, kasancewar yanzu kwallon kafa ta zamanto babbar hanya ta samun arziki a duniya.
Wasu matasa da DW ta zanta dasu wadanda ke samun horo a cibiyar, sun bayyana kudirinsu na samun shiga manya-manyan kungiyoyin kwallon kafa da ke kasashen Turai da zarar sun kammala samun horaswar, kasancewar hatta matasan da ke da karancin ilimin zamani kan samu damar shiga cibiyar, a cewar Shehu Romario da shi ma ke koyar da matasan kwallon kafa a cibiyar.
Masana wasan kwallon kafa a Najeriya irin su Alhaji Kwairanga na ganin babbar dama ce ta samu ga matasan Najeriya mussaman wajen fuskantar wasan kwallon kafar, domin ya zame musu hanyar dogaro da kai. Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na ganin ya kamata hukumomin Najeriya su nazarci hanyoyin da za'a rika sanya matasa domin neman abin kansu, kamar yadda Adamu Babawo ya yi don taimakawa matasan maimakon yadda wasunsu kan zamanto matsala ga al'umma sakamakon rashin aikin yi.