Hillary Clinton ita ce mai dakin tsohon shugaban kasar Amirka Bill Clinton wanda ya yi mulkin kasar daga shekarar 1993 zuwa 2001.
An haifi Hillary a shekarar 1947. Ta shiga neman kujerar shugabancin Amirka karkashin tutar jam'iyyar Demokrat a zaben shugaban kasar na shekarar 2016.