Majalisar dattawan Amirka za ta binciki satar bayanan 'yan siyasa da ake zargin Rasha da aikatawa domin taimakawa wani dan takara a zaben Amirka da ya gabata.
Shugaban Amirka mai jiran gado Donald Trump ya yi watsi da rahoton hukumar leken asiri ta CIA, bisa rawar da Rasha ta taka wajen taimaka masa lashe zaben Amirka da ya gabata. Abin da ya kira soki burutsu na jam'iyyar Democrat da ta sha kaye a zaben, kuma ta ke neman hanyoyin kare faduwar Hillary Clinton a zabe. Kalaman na Trump su na zuwa ne bayan rahoton jaridar Washington Post da ke cewa hukumar CIA ta gano munufar Rasha bisa neman ganin Trump ya lashe zaben bisa satar bayanai da aka yi.
Tun farko wasu 'yan majalisar dattawa daga duk manyan jam'iyyun kasar ta Amirka sun nemi a bankado abin da ya faru kamar yadda Sanata Charles Schumer daga Jihar New York baiyana.