Trump sabon zababben shugaban Amirka na 45 | Shiga | DW | 09.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Shiga

Trump sabon zababben shugaban Amirka na 45

Bayan nasarar bazata da Trump ya yi ta lashe zaben shugaban kasar Amirka, yanzu ya karkata ga neman hada kan Amirkawa

Bayan gagarumar nasarar da Donald Trump ya samu ta bazata, inda ya doke Hillary Clinton a zaben da aka gudanar a Amurika, yanzu hankalinsa ya fara karkarta ga dinke baraka, da kuma rarabuwar kawunan da zaben na bana, ya haddasa a cikin kasar ta Amirka. 
Da yake jawabin yin na'am da zaben da aka yi masa, bayan da ya samu kujeru fiye da dari uku, ita kuma Hillary ta tashi da dari biyu da 'yan kai, Trump ya fara da jinjina wa Hillary dangane da hazakar da ta nuna a yakin neman zaben da suka fafata, musanman ganin cewa, tun kafin a kammala fitar da sakamakon wasu jihohi, ta kira shi ta taya shi murna: 

 

 "Ga duk 'yan jam'iyyar Republican da na Demokrats da kuma wadanda ba sa goyon bayan wata jam'iyya, ina kira gare ku cewa, lokaci ya yi da ya kamata mu hada hannu a matsayin, tsintsiya daya madaurinki daya".

 Daga nan sai sabon zababben shugaban na Amurika Trump ya sake nanata irin ayyukan da zai yi a cikin kasa, domin farfado da samar da ayyukan yi, habaka tattalin arziki, da kula da tsaffin sojoji, yana mai jaddada cewa, gwamnatinsa ta jama'a ce, wadda za ta bai wa dukkan dan kasa damar nuna bajintarsa da kuma cin moriyar hakan. Da ya karkata ga harkokin kasashen waje kuwa, ko da yake bai fadi wata manufa guda daya ba, kamar yadda ya rika yi a lokacin yakin neman zabe, amma ya yi tsokaci kamar haka:

 "Ina mai sheda wa al'umar duniya cewa, duk da yake Amirka ce zan fi bai wa fifiko a kan komi, amma zan yi hulda da kowa bisa adalci".

Ya kuma jaddada cewa, za su dasa da dukkan kasashen da suke da aniyar yin tafiya da Amirka. A nata bangaren, a iya cewa, ta yiwu jimamin yadda wannan sakamakon zabe ya ba Hillary Clinton kunya ne, ya sa a ranar da aka bayyana zaben ba ta ce uffan ba ga magoya bayanta, illa kawai, ta tura wanda ya jagoranci yakin neman zabenta din ne, Mr John Pedosta zuwa helkwatarta da ke birnin New York, inda ya sheda wa dunbin masoyanta da suka yi zugum, wasu na kuka, huska a daure, cewa, su tafi gida, uwargida Hillary ba za ta samu yin wani jawabi ba. Shakka babu, ga duk wanda yake bin diddigin siyasar Amirka, zaben Donald Trump, tamkar wani gagarumin sako ne aka aika wa gwamnatin Obama mai barin gado cewa, Amirkawa suna bukatar canji, sun gaji da marawa 'yan siyasa baya, musanman ganin cewa Trump dan kasuwa ne, wanda bai taba yin wani takamaiman aikin gwamnati ko kuma na soja ba. Kazalika, zaben tamkar wani sako ne mai karfi da 'yan Republican suka aika wa shugabannin jam'iyarsu cewa, rashin marawa Trump da suka yi, bai hana shi damar zama shugaban Amirka na 45, mai jiran-gado ba.

 Shima dai Dr. Muhammad Kabir Hassan kenan, wani masanin al'amuran siyasa ya yi karin haske kan fa'idar nasarar da Donald Trump ya samu kan siyasarv kasar ta Amirka a nan gaba: 

"Tabbas duk da sabanin da Trump ya yi da jiga-jigan  jam'iyyarsa ta Republican, wani abin da zai iya taimaka ma gwamnatinsa, shi ne cewa, a sakamakon zaben na jiya, yanzu majalisar dokoki da ta dattawa, suna hannun jam'iyarsa". 

Yanzu haka dai, Amirkawa da sauran al'umar duniya, sun zuba idanu, su ga ga ko Trump zai iya aiwatar da alkawurran da ya yi a lokacin yakin neman zabe, ko kuma a a. Abu daya dai da akasarin masharhantan suke nunawa a kasar ta Amirka, shi ne, ga dukkan alamu, mai yiwuwa Trump zai warware wasu daga cikin ayyukan da Shugaba mai barin gado, Barak Obama ya yi, musanman a bangaren kiwon lafiya, da kuma aniyar da Obaman ya nuna, ta yin sassauci, ga 'yan cirani masu zama kasar nan, ba bisa ka’ida ba.

Sauti da bidiyo akan labarin