Clinton ta magantu kan nasarar Trump | Labarai | DW | 09.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Clinton ta magantu kan nasarar Trump

'Yar takarar jami'iyyar Democrats da ta sha kaye a zaben Amirka Hillary Clinton ta bayyana cewa ba abu ne mai dadi ba faduwa a zabe.

Historisch: Barack Obama und Hillary Clinton

Shugaban Amirka Barack Obama da 'yar takarar da ta sha kaye Hillary Clinton

Clinton ta ce tana fatan wanda ya samu nasara a zaben na Amirka abokin hamayyarta Donald Trump  zai ci gaba da tafiyar da kasarsu bisa natija mai kyau. Clinton ta bayyana hakan ne yayin da take jawabi ga dinbin magoya bayanta a wani taron manema labarai da ta gudanar da yammacin wannan Laraba. Shima a nasa jawabin shugaban Amirkan mai barin gado wanda shima yake zaman dan jam'iyyar ta Democrats, Barack Obama ya nunar da cewa faduwa a zabe abu ne mai matukar ciwo sai dai yana gayyatar Trump zuwa fadar gwamnati ta White Hause, kana yana fatan mika mulki cikin kwanciyar hankali.