1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi mai amfani da hasken rana

July 15, 2020

Wani matashi da ya kammala karatun digirinsa a jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto a Najeriya, ya rungumi sana'ar samar da wuta lantarki ta bangaren hasken rana wato Solar domin dogaro da kansa.

https://p.dw.com/p/3fKHX
Nigeria Solar Innovation in Sokoto
Matashi Ibrahim Abubakar Riskuwa mai samar da hasken wutar lantarki da hasken ranaHoto: DW/M. A. Sadiq

To shi dai wannan matashi mai suna Ibrahim Abubakar Riskuwa ya bayyana cewa ya yanke shawarar fara wannan sana'ar ta kir-kira da kuma sarrafa hasken rana zuwa hasken wutar lantarki tsawon shekaru biyun da suka gabata, bayan ya kammala karatunsa na jami'a.

Koda yake bayan da likkafa ta ci-gaba, matashin ya bude kamfaninsa da ke samarwa da kuma aikin saka hasken lantarkin na sola a gidajen mabukata, sai dai ya ce sana'ar tattare take da dimbin kalubalen da suke ta kokarin shawo kan su.                                                                                              

Yanzu haka dai kamfanin wannan matashi na samar da hasken lantarki, cike yake da matasa masu aikin sakawa a gidaje. Tuni dai al'umma ke ci gaba da yabawa wannan matashi sakamakon samar da hasken wutar lantarkin da yake yi ta hanyar amfani da hasken rana, musamman a irin wannan lokaci da hasken wutar lanatarkin a Najeriya ke kwan gaba kwan baya.