1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Matashin da ya yi injin kyankyasar kaji

March 9, 2022

Wani matashi a jihar Katsina, ya kirkiro injin kyankyasar kaji me amfani da wuta da gas da kuma hasken rana.

https://p.dw.com/p/48DYQ
Najeriya I Kaduna
Gidan gona kaji a Kaduna, NajeriyaHoto: DW/J.-P. Scholz

Matashin mai suna Muhammad Usman dake cikin Birnin Katsina ya kama wannan sana'ar bayan da ya kammala karatunsa na diploma amma babu aikin yi, kuma ya ce a yanzu haka ya kera injinan sama da 30, kuma da ya kera ake saye. A cewarsa sabida bukatar injin da ake da ita, ya dauki matasa kusan 10 aiki. Usman ya ce ya samu tarin nasarori sakamakon kirkiro wannan inji kyankyasar kajint, sai dai kuma ba a rasa kalubale kamar yadda tsadar kayayyakin hada injin kyankyasar kajin ya fi ci masa tuwo a kwarya. Daga karshe Usman ya ce babban burinsa shi ne ya bude ma'aikatar da zai rika kera injinan kyankyasar kajin, domin ya samu damar daukar matasa masu yawa aiki saboda yanzu wani dan wuri ne aka kebe masa a farfajiyar gidansu yake aikin kera injinan.