1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashiya mai sana'ar dambun nama

June 2, 2021

Matashiyar ta ce ta fara sana'ar ne a gidan mahaifinta kuma tana sayarwa a cikin birnin Katsina, sai dai daga bisani sana'ar ta habaka inda yanzu take kai dambun naman jihohi dabam-dabam.

https://p.dw.com/p/3uMuN
Symbolbild Pferdefleischskandal
Hoto: Fotolia/hjschneider

Matashiyar mai suna Zainab Lawal Abdulkadir na yin dambun naman da kaji, kuma ta ce ta shiga wannan sana'ar da kafar dama ta la'akai da irin nasarorin da ta samu, koda yake hakan ba yana nufin ba ta fuskantar kalubale ba.

Ganin Zainab tana matashiya ta kama wannan sana'a ta dambun nama kuma ta yi sa a sana'ar ta karbeta, hakan ya sa ta yi amfani da damarta wajan nusar da 'yan uwanta mata, kan su tashi su nemi na kansu. A cewar Zainab a yanzu ba ta jiran sai an ba ta kafin ta yi wa kanta da ma dangi hidima.