1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yunkurin sulhu don warware takkadama a Sudan

Abdul-raheem Hassan AMA(ATB)
June 9, 2022

Bayan shafe watanni takwas ana takun sakar siyasa, shugabannin gwamnatin mulkin soji a Sudan sun fara tattaunawa da kungiyoyin 'yan adawa da farar hula don samun sulhu.

https://p.dw.com/p/4CU95
Sudan |Shugaban Majalisar soji | Janar Abdel Fattah al-Burhan
Sudan |Shugaban Majalisar soji | Janar Abdel Fattah al-BurhanHoto: Marwan Ali/AP/dpa/picture alliance

Sabuwar tattaunawar ta zo ne bayan da shugaban mulkin soja Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya janye dokar ta baci da aka kafa tun bayan juyin mulkin shekarar 2021 da ya bashi damar hawa karagar mulki. Ya kuma saki masu zanga-zanga 125 tare da yin kira da a yi tattaunawa mai ma'ana da za ta kawo kwanciyar hankali a kasar. 

Ga dukkan alamu Janar al-Burhan ya sauya matsayinsa na farko na cewa zai sauka ne kawai da zarar an kafa sabuwar gwamnati. Wasu 'yan fafutuka kamar Mohamed Yousif Almustafa na ganin matakin da wata fuska "Burhan yana kokarin sanya rudani ne a cikin dakarun juyin-juya hali da cewa yanzu mun ba ku isasshen 'yanci, mun sako duk wadanda ake tsare da su, don haka ku zo ku tattauna da mu."

Karin Bayani: Rikicin Darfur na Sudan na daure kai

Duk da cewa kungiyar fafutukar 'yanci da kawo canji a Sudan, ta tabbatar da samun takardar gayyatar jiga-jigan sulhu irin tarayyar Afira, hadin gwiwar da Majalisar Dinkin Duniya da hukumar raya ci gaba na taimawa Sudan wajen shiga tsakanin gwamnati da kungiyoyin da basa jituwa, kungiyar FFC ta ce ba za ta halarci zaman taron ba saboda tattaunawar ta kunshi bangaren adawa da ke goyon bayan juyin mulki a Sudan.

Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Oktoban 2021 lokacin da sojoji suka hambarar da gwamnatin rikon kwarya karkashin Abdalla Hamdok, tare da maye gurbinta da majalisar mulkin soji karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan, fararen hula sun fantsama kan tituna, suna kira ga a dawo da mulkin demokradiyya. An kashe masu zanga-zangar 100 tare da jikkata sama da 5,000. "Babu wanda aka zarga da aikata wadannan laifuffuka. Kuma ba alamar sassauci a mulkin danniya" in ji Human Rights Watch.

Sudan Khartoum | Masu bore | Zanga-zanga
Sudan Khartoum | Masu bore | Zanga-zangaHoto: AFP/Getty Images

Wannan ya sa Mohammed Elnaiem, ke ganin 'yan Sudan ba za su taba yarda da yunkurin tattaunawar ba muddin ba bi wasu matakai ba. "Idan sojoji suna son su sami ko wane irin ra'ayi a cikin wani nau'i na ci gaba ga Sudan, to yakamata su gano abubuwa biyu ko uku. Na farko, yadda za su yi watsi da mamayar da suke yi a kan muhimman sassa na Sudan. Tattalin arzikin Sudan da kuma mika shi a hannun jama'a. Na biyu shi ne binciken laifuffukan da aka yi tare da kafa kwamitin gaskiya da sulhu na laifukan da sojoji da 'yan sanda da sauran hukumomi daban-daban na kasar suka aikata. Na uku zana taswirar ruguza duk wasu 'yan bindiga da kuma tsame su daga siyasa."

Karin Bayani: An yi kiran janye dokar ta-baci a Sudan

Tun bayan ayyana dokar ta baci a shekarar 2021, kasashen duniya sun dakatar da kudaden agaji ga kasar Sudan a sakamakon haka matakin da ya kara yawan bashin kasa da kasa, abinda ya jefa al'ummar kasar miliyan 45 cikin wani hali. Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ta yi gargadi kan matsalar karancin abinci da ke kara kamari a wurare 20 da ake kira "wuri da ake fama da yunwa," ciki har da Sudan da Sudan ta Kudu. Hukumar tana tsammanin kashi 30% na yawan jama'a, ko kuma mutane miliyan 10.9, za su bukaci "tallafin gaggawa a wannan shekara, adadi mafi girma a cikin shekaru goma da suka gabata.  ko da yake ana danganta tsananin halinda kasar ke ciki da annobar corona da kuma yakin Rasha da Ukraine.