1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi kiran janye dokar ta-baci a Sudan

May 29, 2022

Bayan kwashe watanni karkashin dokar ta-baci a Sudan, an bayyana bukatar sakar wa al'uma mara domin samun ci gaba da harkokinsu na walwalar da suka saba a fadin kasar.

https://p.dw.com/p/4C0zA
Sudan politische Krise | Abdel Fattah al-Burhan
Hoto: Mahmoud Hjaj/AA/picture alliance

Majalisar tsaro a Sudan ta bayar da shawarin janye dokar ta-baci da gwamnatin soji ka kafa a fadin kasar bayan kwace iko da ta yi a bara.

Bangaren tsaron na Sudan ya kuma nuna bukatar sakin duk wadanda gwamnati ke tsare da su bayan yamutsin da aka samu sakamakon sauyin gwamnati da aka samu a baran.

A ranar Lahadi ne dai shugaban gwamnatin Sudan din Janar Abdel Fatah al Burhan, ya jagoranci taron da ya maida hankali kan batutuwan tsaron kasar bayan kifar da gwamnatin dimukuradiyya a ranar 25 ga watan Oktoba.

A gefe guda kuma, a yau ne jakadan Majalisar Dinkin Duniya a kasar Volker Perthes ya nuna bacin ransa game da kisan wasu mutum biyu, a wani yunkurin tarwatsa masu zanga-zangar goyon bayan dimukuradiyya da jami'an tsaro suka yi.