1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Darfur na Sudan na daure kai

Abdourahamane Hassane MA
April 28, 2022

An sake samun munanan tashe-tashen hankula tsakanin kabilu masu adawa da juna a yankin Darfur na kasar Sudan. Sabbin tashin tashinar na nuni da kara tabarbarware al'amura.

https://p.dw.com/p/4AZB5
Sudan West Darfur | Rauchwolken im Abu Zar Camp
Hoto: AP/picture alliance

Akalla mutane 200 ne suka mutu sannan kusan 100 suka jikkata, tare da dubun dubatar mutane da suka guje wa fadan. Rikicin da ba a warware ba a Darfur, na ci gaba da lakume rayukan mutane da dama. Tashin hankalin ya faro ne a ranar Juma'ar da ta gabata lokacin da wasu 'yan bindiga Larabawa dauke da makamai suka kai hari a kauyukan 'yan kabilar Massalit, 'yan tsiraru na Afirka.

A cewar rahotanni, maharan sun kai hare-hare a kan asibitoci da dama a yankin wanda suka lalata. Maharan Larabawa na kallon hare-haren nasu a matsayin ramuwar gayya ga mutuwar wasu 'yan kabilar biyu da suka mutu ba da jimawa ba a wata takaddama da wasu al'ummar Afirkan mazauna yankin. Rikicin dai na nuni da rigingimun da har yanzu ba a warware su a Sudan ba, na kara ta'azara a kan dalilai da dama daga cikin su har da na canjin yanayi.

Rikicin Darfur ya samo asali ne daga fari da yunwa da aka yi a kasar Sudan tsakanin shekara 1983 zuwa 1984, wanda dubban daruruwan mutane suka rasa kayansu, musamman kungiyoyin Larabawa da abin ya fi shafa, yayin da kungiyoyin jama'ar Afirka wadanda makiyaya ne suka rikide zuwa ‘yan kasuwa suka kuma mamaye harkokin kasuwancin cikin kankanin lokaci.

Sudan | El Geneina | Haupstadt West-Darfur
Hoto: AFP

A farkon shekarun 2000, shirin wanzar da zaman lafiya tsakanin sassan kasar biyu da suka rabu, wato arewaci da Sudan ta Kudu, ya mayar da hankali kan warware rikicin ta hanyar siyasa. Sai dai babban kuskuren da aka yi shi ne na ware yankin Darfur wanda ba a hada shi ba a tattaunawar.

Shugaban Sudan na lokacin wanda aka hambare a shekarar 2019 Omar al-Bashir, ya dauki matakin soji kan ‘yan tawayen Larabawa na Janjaweed wadanda suka yi amfani da yakin wajen aikata kisan gilla a kan fararen hula. 

Sojojin da suka yi juyin mulki a bara wadanda suka zo kan karagar mulki, sun gaza daukar mataki a kan wadanda ke da hannu a rikicin na Darfur saboda akwai da yawa daga cikin su har ma a jagoran sojojin Janar Al Burhan masu hannu a kisan gillar na yankin Darfur.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, yakin na Darfur ya lakume rayuka kusan dubu 300,000m yayin da mutane miliyan daya da rabi ne ke ci gaba da zama a sansanonin 'yan gudun hijira.