1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkokin siyasa a masar sun fara daukar zafi

ibrahim saniJuly 20, 2005

Harkokin siyasa a kasar Masar naci gaba da tabarbarewa sakamakon gyaran fuska na yar zagalin zagalin da aka gudanar a kundin tsarin mulkin kasar

https://p.dw.com/p/Bvam
Hoto: dpa - Bildfunk

A yayin da lokacin zaben shugaban kasa ke kara karatowa a kasar ta masar, da yawa daga cikin jamiyyun adawa da suka ci alwashin kalubalantar shugaba Mubarak a wannan zabe a yanzu haka sun fara jada baya daga matakin da suka dauka da tun da farkon fari.

Duk da cewa wasu jamiyyun sun fara daukar matakin kin tsayar da dan takara a mukamin shjugaban kasar, wasu jamiyyun kuma naci gaba da tunanin daukar matsaya guda game da wannan abu.

A cewar daya daga cikin shugabannin jamiyyun adawar kasar wato Said Al Said, cewa yayi da yawa daga cikin jamiyyun adawar sun dauki wannan matakin ne bisa hasashen cewa akwai alamar yar zagalin zagalin a cikin zaben da za a gudanar a watan satumba na wannan shekarar.

Said Al Said yaci gaba da cewa, jamiyyun adawar kasar sun bukaci a gudanar da gy