Hariri ya nemi ′yan Lebanon su fifita kasarsu | Labarai | DW | 23.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hariri ya nemi 'yan Lebanon su fifita kasarsu

Saad al-Hariri ya sake jaddada bukatar ganin Lebanon ta janye kanta daga duk wani rikici a yankin ba kawai ta fatar baki ba har ma da aikace.

Firaministan kasar Lebanon Saad al-Hariri ya yi jawabi a wannan rana ta Alhamis inda ya yi kira ga al'ummar kasar su zama masu fifita Lebanon gaban wasu batutuwa da suka shafi yankin da kasarsu take.

Hariri na jurwaye mai kamar wanka ne kan dalilai da suka sanya ya dauki mataki na cewa ya ajiye mukaminsa ranar 4 ga wannan wata lokacin ya na kasar Saudiyya mai karfin fada aji kuma abokiyar gabar kasar Iran.

Hariri ya sake jaddada bukatar ganin Lebanon ta janye kanta daga duk wani rikici a yankin ba kawai ta fatar baki ba har ma da aikace. A cewarsa zaman lafiya shi ne babban abin da suka sanya a gabansu kuma shi ne burinsu.