Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Wasu hare-haren bama-bamai na kunar bakin wake da aka Kai a jihohin Yobe da Gombe da ke Tarayyar Najeriya a jajiberin Sallah da kuma ranar Sallah, sun kara jefa al'ummar kasar cikin alhini da fargaba.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki a karo na farko a jihar Yobe, inda ya kaddamar da wasu ayyuka da su ka shafi inganta tsaro da kuma farfado da harkokin rayuwa da tattalin arzikin kasa.
Wani hadari mai muni da ya auku a yankin arewa maso gabashin Najeriya ya salwantar da gomman rayuka a wannan Talata. Hadari ne da ya hada wasu motoci biyu.
Al'ummar arewa maso gabashin Najeriya na martani bayan ikirarin Shugaba Buhari na cewa gwamnatinsa ta murkushe kungiyoyin ta'adda irin su Boko Haram a shiyyar.
Kazamin hari da mayakan ISWAP suka kai kan 'yan agaji a Monguno na jihar Bornon Najeriya ya haifar da lalata motoci guda 22 da ake aikin jin kai da su. Sannan ana zargin mayakan da tafiya da wasu motocin jami’an tsaro.