1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe sojojin Najeriya

Binta Aliyu Zurmi
June 28, 2020

Rahotanni daga Najeriya na cewar akalla jami'an sojan kasar 9 da wasu mayakan sa-kai biyu ne aka kashe a wani harin kwantan bauna da aka yi wa ayarin motocin farar hula a kauyen Komala da ke kusa da Damboa.

https://p.dw.com/p/3eTOF
Nigeria Islmischer Staat in West Afrika ISWAP Truck
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Jami'an tsaro a yankin sun tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP aukuwar wannan lamari, inda suka ce mayakan sun bude wa jerin motocin farar hula sama da dari wuta tare wa jefa musu ababe masu fashewa. 

Ya zuwa yanzu dai ba a sanda inda wasu daga cikin fararen hular da ke cikin ayarin motocin suka shiga ba bayan da aka kai harin.