Harin ta′addanci a Jamhuriyar Nijar | Siyasa | DW | 20.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Harin ta'addanci a Jamhuriyar Nijar

A Jamhuriyar Nijar wani jami'in tsaro guda ya rasa ransa yayin da wasu biyu kuma su ka jikkata, sakamakon harin da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba su ka kai.

Harin dai an kai shi ne a wani gari mai suna Banibangou da ke da kimanin nisan
kilomita 250 da Yamai babban birnin kasar cikin gundumar Wallam. Hukumomin jihar sun ce a halin yanzu komai ya koma dai-dai yayin da sojoji ke ci gaba da aikin farautar maharan wadanda aka ce sunfito ne daga kasar Mali. Bayanai dai na nuni da cewa maharan su kimanin 70 a kan babura da kuma mota sun kai harin nasu ne a wani barikin jami'an tsaro na jandarma da ke garin na Banibangou.

Artabu da jami'an tsaro

Bayanai sun nunar da cewa an yi mummunan artabu tsakanin maharan da jami'an tsaron kasar wadanda suka ja daga a gurare daban-daban bayan da suka samu labarin zuwan maharan. Saidai maharan sun samu nasarar shiga garin ta wata hanya daban abin da ya basu damar yin barna a barikin jami'an jandarman Banibangou, kafin sojojin kasar su kai musu dauki. Honnorable Karimu Bureima dan majalisar dokoki daga gundumar ta Wallam ya ce hare-haren ba su da nasaba da wasu kungiyoyin 'yan ta'adda, inda ya ce matsala ce da ta dade kuma gwamnati ta san da ita sai dai ta gaza yin komai domin shawo kanta.

A nasa bangaren da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar sojojin Jamhuriyar ta Nijar ya ce baya ga motar da maharan suka kona sun kuma yi nasarar tserewa da mota guda, sannan kuma sun jikkata jami'an tsaron Nijar din biyu.

Harin ba shine karon farko ba

Wanann dai shine hari karo na hudu cikin kasa da wata guda, da aka kai a cikin gundumar ta Wallam ba tare da wata kungiya ta dauki alhakin kaiwa ba. Tuni dai wata tawagar ministocin kasar da magabatan jihar Tillaberi ta isa zuwa garin na Banibangou domin ganewa idanunta lamarin.