Harin sojin Najeriya ya halaka matar Shekau | Labarai | DW | 25.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin sojin Najeriya ya halaka matar Shekau

Rundunar sojin Najeriya ta ce tana gudanar da bincike don tantance wani rahoton da ke cewa wani harin bam da ta kai kan taron mayakan Boko Haram ya halaka daya daga cikin matan shugaban kungiyar Abubakar Shekau.

A cewar rundunar a makon da ya gabata ta kai wani hari ta sama kan mayakan a yayin da suke ganawa a wani gari da ke yankin Konduga na jahar Borno. Sanarwar ta kara da cewa harin ya halaka mayakan kungiyar da dama tare da haifar da gobara.

 Kakakin sojan saman kasar Olatokunbo Adesanya ya ce, su na kokarin sanin ko wata mata mai suna Firdausi da ke cikin wadanda harin ya halaka lallai mai dakin shugaban kungiyar ta Boko Haramun ce.

Adesanya ya ce, bayanan da suka samu ya nuna cewa, Firdausi ta maye gurbin mijinta inda ta ke wakiltar Shekau a duk wani taro da mayakan da ke biyayya ga shugaban kungiyar da ayyukanta ya haifar da asarar rayukan mutane da dama a jihohin Arewa maso gabashin Najeriya.Ana kyautata zaton su na cikin irin wannan zama a lokacin da sojojin na Najeriya suka afka musu.