Harin roka kan wata mota a Ukraine | Labarai | DW | 22.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin roka kan wata mota a Ukraine

Rasha ta ce ta kadu bayan da ta samu labarin wani hari na roka da aka kai kan wata mota kirar safa a gabashin Ukraine wanda ya yi sanadin rasuwar mutane da jikkata wasu.

Ministan harkokin wajen Rasha din Sergei Lavrov ya ce wannan farmaki da aka kai abu ne da zai tunzura mutane kana zai yi kafar ungulu da irin kokarin da ake yi wajen wanzar da zaman lafiya tsakanin Ukraine din da Rasha.

Rasha dai ta ce sojin Ukraine ne ke da hannu wajen harba rokar da ya tarwatsa motar da sanyin safiyar yau, yayin da mahukuntan Ukraine suka ce harin aiki ne na 'yan awaren gabashin Ukraine da ke gwagwarmaya da makamai wanda Rasha ke marawa baya.