Harin kunar bakin wake a Bornon Najeriya | Labarai | DW | 30.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake a Bornon Najeriya

Tashin wani bam da aka samu a wani masallaci a birnin Maiduguri na jihar Bornon Najeriya ya yi sanadin rasuwar mutane da dama.

Shaidun gani da ido suka ce suna zaton dan harin kunar bakin wake ne ya tashi bam din da ke jikinsa daidai lokacin da aka fara sallar la'asar a wani masallaci daura da wata kasuwa a garin na Maiduguri, kuma baya ga wanda suka rasu an samu wasu da dama da suka jikkata.

Wannan sabon harin na zuwa ne bayan da wasu da ake zaton 'yan Boko Haram ne suka kai wasu jerin hare-hare na bam a Maidugurin cikin daren jiya Juma'a zuwa wayewar garin Asabar din nan.

Hakan dai na faruwa ne kwana guda bayan da aka rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin sabon shugaban kasar, wanda a jawabinsa na kama aiki ya lashi takobin ganin bayan kungiyar.