Harin kunar bakin wake a Afghanistan | Labarai | DW | 26.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake a Afghanistan

Wani harin kunar bakin wake da aka nufi kaiwa a kan ofishin jakadancin kasar Turkiya da ke kusa da ofishin jakadancin Iran a kasar Afghanistan ya hallaka mutane biyu.

Rahotanni sun nunar da cewa tuni kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin bam din da ya tashi a kofar ofishin jakadancin Iran, inda ta ce ta kudiri kai harin ne a kan ayarin motocin wasu 'yan kasashen ketare. Mataimakin ministan cikin gida na kasar ta Afghanistan Mohammad Ayub Salangi ya tabbatar da faruwar al'amarin. Jami'an 'yan sandan kasar sun ce daya daga cikin wadanda suka rasa rayukansu dan kasar Turkiya ne kana gudan kuma dan Afghanistan din ne da ya zo wucewa.