Harin dan bindiga a birnin Moscow | Labarai | DW | 19.12.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin dan bindiga a birnin Moscow

Wani dan bindiga ya buda wuta a kasar Rasha tare da hallaka jami'in tsaro daya da raunata jama'a a dab da harabar ma'aikatar leken asirin kasar da ke tsakiyar birnin Moscow.

Rahotanni sun shedawa kafafen yada labarai cewa jami'an tsaro sun bindige maharin, sai dai daga nasu bangare har yanzu hukumomin ba su yi wani karin bayani ba dangance da kai harin, to amma kuma wata majiya ta sheda da cewa ana ci gaba da bincike domin gano wanda ya kai harin, kana shedu sun ce an ga jami'an tsaro sun killace wurin da aka yi harbe-harben, lamarin da kuma ya haifar da cinkoson ababen hawa. A shekararun da suka gabata dai kasar ta Rasha ta sha fuskantar hare-hare makamancin wannan, wanda aka alakanta da yakin da aka sha yi a yankin Ceceniya masu neman ballewa.