Harin bam ya kashe mutane 5 a Maiduguri | Labarai | DW | 12.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam ya kashe mutane 5 a Maiduguri

 A Najeriya wasu mutum biyar sun mutu bayan fashewar da aka samu a sansanin 'yan gudun hijra da ke kusa da garin Gwoza a jahar Borno a yammancin jiya Litinin a daidai lokacin da likitocin MSF ke tsakiyar aikinsu.

A cewar kanar Oynema Nwachukwu kakakin rundunar soji da ke a birnin Maiduguri, harin ya auku ne a yayin da jami'an likitocin kungiyar agaji ta MSF ke tsakiyar aikin kulawa da al'ummar da ke rayuwa a sansanin.Da farko acewar jami'an kungiyar an yi tunanin harin kunar bakin wake aka kai, amman bayan bincike an gano ba haka batun ya ke ba, kawo yanzu ba a tabbatar da ko dasa abin fashewar aka yi ba a cikin sansanin. Akwai wadanda ake bai wa kulawa a asibiti a sanadiyar raunin da suka samu daga fashewar.

Hakazalika an tabbatar da mutuwar wasu sojoji biyu a ranar Lahadin da ta gabata bayan da motar da suke tafe a ciki ta bi ta kan wasu abubuwan fashewa da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram da danawa a hanyar Damboa na birnin Maidugurin jahar Borno a arewa maso gabashin Najeriya mai fama da ayyukan ta'addanci.