Harin bam ya hallaka 'yan Shi'a a Kano | Labarai | DW | 27.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam ya hallaka 'yan Shi'a a Kano

Rahotanni daga jihar Kano na cewar tashin bam ya hallaka wasu mabiya tafarkin Shi'a a Kano lokacin da suke wani tattaki zuwa birnin Zariya da ke jihar Kaduna.

Shugaban mabiya Shi'a din da ke na Kano Muhammad Turi ya shaidawa wakilinmu na Kano Nasir Salisu Zango cewar mutane 21 ne suka rasu sakamakon harin kuma wasu da dama sun jikkata.

Rundunar 'yan sandan Kano da ta tabbatar da wannan harin yanzu haka ta ce ta na cigaba da gudanar da bincike. Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dau alhakin kai wannan hari, sai dai kungiyar nan ta Boko Haram ta sha daukar alhakin kai harin bam a garin na Kano.