Harin bam ya hallaka mutane a Kano | Labarai | DW | 19.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam ya hallaka mutane a Kano

Wani harin bam da aka kai unguwar Sabon Garin Kano a daren jiya Lahadi ya yi sanadiyyar rasuwa mutane kimanin biyar tare da jikkata wasu da dama.

Harin wanda na kunar bakin wake ne ya auku a unguwar Sabon Garin Kano, a kan titinn nan naMiddle Road daura da Gold Coast da ke da yawan mashayu da kuma otal-otal.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ta Kano Aderinle Shinaba da ya tabbatar da harin ya ce an kai shi ne da wata mota kirar Golf wadda aka makareta da bama-bamai kuma kimanin biyar ne suka mutu ciki kuwa wata yarinya 'yar shekaru sha biyu da haihuwa.

Ya zuwa yanzu dai ba wanda ya dau alhakin kai harin na daren jiya wanda jihar ta Kano ta jima ba ta ga irinsa ba sai dai kakakin rundunar 'yan sandan Kano din Musa Magaji Majiya ya shaidawa wakilinmu na Kano Nasir Salisu Zango cewar tuni sun fara gudanar da bincike da gano wanda ke da hannu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balarabe